Annobar sanƙarau ta kashe mutum 140 a Nigeria

Doctor examining a patient Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A jihar Zamfara ce annobar sanƙarau ɗin ta fi ƙamari don kuwa kusan duk ƙananan hukumomin jihar na fama da cutar

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar kimanin mutum 140 sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a wasu jihohin ƙasar.

Ta ce a jihar Zamfara ce cutar ta fi ƙamari, inda ta yi sanadin mutuwar mutum 86, baya ga ƙarin wasu 590 da ke jinya sakamakon kamuwa da sanƙarau.

Daraktan taƙaita yaɗuwar cutuka a ma'aikatar lafiya ta tarayyar Nijeriya, Dr. Nasiru Sani Gwarzo ya ce jihohin da cutar ta ɓulla sun haɗar da Zamfara da Sakkwato da Neja da Kano da kuma babbar birnin Abuja.

A cewarsa sun tabbatar da mutuwar mutum 10 a jihar Sakkwato da kuma wasu 32 a jihar Neja, ko da yake goma sha shida ne aka tabbatar sun mutu sakamakon wannan annoba.

Ana alaƙanta cutar sanƙarau da yanayin zafi mai tsanani da kuma kwanciya a cikin muhalli mai cunkoso ba tare da kai komon iska ba.

Dr. Nasiru Gwarzo ya ce suna ci gaba da tattara alƙaluma, don haka mai yiwuwa adadin ka iya ƙaruwa.

Ya ce gwamnatin Nijeriya tana ɗaukar matakai don ganin cutar ba ta ci gaba da bazuwa zuwa sauran sassan ƙasar ba.

Daraktan ya ce tun a bara, gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sanar da Nijeriya game da ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙasar, da kuma yiwuwar bazuwarta zuwa Nijeriya.

Ya ce ko da an yi wa mutum riga-kafi, to akwai buƙatar a guji zama cikin yanayin cunkoso a gidaje da wuraren aiki don kare kai daga kamuwa daga sanƙarau.

Labarai masu alaka