Yunwa na yi wa yara ƙanshin mutuwa

Somaliya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yara karban abinci daga hukumar bada agaji

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce fiye da wata guda kenan da aka ayyana fari a kasar Sudan Ta Kudu, amma lokaci na ci gaba da kurewa ba tare da yaran da ke cikin halin matsananciyar yunwa sun samu taimakon da suke bukata ba.

Fiye da yara miliyan daya ne suke cikin halin ha'ula'i a kasashen arewa maso gabashin Najeriya da Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma Yemen sakamakon yaki da ya wargaza rayuwarsu.

Daraktar kula da bayar da agajin gaggawa ta UNICEF Manuel Fontaine, ta ce ''Yara ba za su iya jira sai an sake ayyana yunwa sannan mu dau mataki ba."

Ya kara da cewa, "Mun yi koyi da abin da ya faru lokacin da aka fuskanci matsananciyar yunwar a Somaliya a shekara ta 2011, wanda kafin a bayar da sanarwar farin, yara da dama sun riga sun mutu. Hakan bai kamata ya sake faruwa ba.''

Hukumar ta UNICEF ta ce wasu yara miliyan 22 suna fama da yunwa da rashin lafiya da rashin muhalli da kuma rashin zuwa makaranta a kasashen hudu, inda kusan miliyan 1.4 daga cikin su ke fuskantar hadarin mutuwa a shekarar 2017 sakamakon yunwa.

UNICEF na bukatar kusan dala miliyan 255 domin bai wa yara abinci da ruwa da kiwon lafiya da ilimi da kuma tsaro har tsawon watanni masu zuwa.

Fiye da dala miliyan 81 daga kudin za a yi amfani da su ne domin kare yara daga matsalar tamowa da samar musu abincin da ke da ingantaccen sanadari.

Za a yi amfani da karin dala miliyan 53 wajen kiwon lafiya da ya hada da allurar rigakafin cututtuka, yayin da dala miliyan 47 za a yi amfani da ita wajen samar da ingantaccen ruwan sha da tsabtataccen muhalli.

Sauran kudi zai taimaka wajen kare yaran da rikici ya shafa kuma a basu ilimi mai inganci. Za a kuma baiwa iyalai mafiya rauni taimako.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane na jiran abinci

Hukumar ta UNICEF na aiki tare da kawayenta a cikin kasashe hudu domin daukar mataki kan yunwa da ke barazana a kasashe da hana yaduwarta:

  • A arewa maso gabashin Najeriya, UNICEF za ta bai wa mutane miliyan 3.9 agajin gaggawa na kiwon lafiya a wannan shekarar, da ba yara 220,000 'yan kasa da shekara biyar maganin tamowa. Kuma mutum fiye da miliyan daya za su samu ruwan sha.
  • A Somaliya, UNICEF za ta taimakawa yara miliyan 1.7 'yan kasa da shakara biyar, ta bai wa 277,000 maganin tamowa ta hannun cibiyoyin kasar.
  • A Sudan ta kudu, UNICEF tare da kawayenta za su bai wa mutane 128,000 taimako a yunkunan da ke fama da yunwa da suka hada da yara 30,000 'yan kasa da shekara biyar.
  • A Yemen UNICEF ta kara ayyuka domin daukar mataki a kan tamowa ta cibiyoyin kiwon lafiya da ma'aikatan kiwon lafiya domin kai wa wasu al'umomin kiwon lafiya da wasu da suka rasa muhallinsu.

Hukumar tana tallafawa yara dama masu fama da tamowa da taimaton kudi da ruwa da ayyukan tsabta, har da samar da ruwa mai tsabta da kayayyaki da kuma kiwon lafiya.

Misis Fontaine ta ce''Yayin da tashin hankali da yunwa da kishirwa ke sa mutane gudun hijira, tamowa za ta ci gaba da karuwa ba a wannan kasashe hudu ba kawai, har da ma tafkin Chadi da yankin kusurwar Afrika."

Idan Kungiyoyin agaji ba su samu kudaden da suke bukata domin kai wa ga masu rauni ba, to za a iya rasa rayuka.

Labarai masu alaka