Kun san halin da rikicin satar shanu ya jefa Zamfara?

Jihar Zamfara Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Manoma ba sa iya yin noma, fulani ba sa iya zuwa masallacin jumma'a da kasuwanni saboda yawan hare-hare.

Al'ummar jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya sun shiga mummunan hali a shekarun baya-bayan nan, sakamakon rikicin ɓarayin shanu wanda ya yi sanadin asarar ɗumbin rayuka da dukiya.

Rikicin wanda ya fi karkata tsakanin ɓarayin shanu da akasari 'yan banga ya kuma tilasta wa mutane a yankunan karkara da dama a cikin jihar tserewa daga gidajensu.

Malama Zainabu Abu wata mata ce da ta shaida wa BBC cewa da rikicin ya jefa su cikin matsananciyar wahala inda aka bar mata da tarin marayu.

Ta ce '' Akwai lokacin da aka kashe mutane 10 lokaci ɗaya, mace mai ciki garin gudun 'yan fashi ciki ya zube, mace mai goyo ta fadi ta karye, ga marayu an bar wa mata, gaskiya mun sha wahala.''

Malam Ibrahim Wakala Liman mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya ce ɗaruruwan mutane sun salwanta saboda hare-hare da aka riƙa kai wa mutane da dabbobi a gonaki, da hanyoyi har ma da gidajen jama'a.

''Abin ya yi ƙamari sosai har ta kai ga fulaninmu ba sa iya fita masallacin Juma'a da kasuwanni, manomanmu ba sa iya shiga cikin daji su yi noma cikin nutsuwa''

Ya ce an yi asarar rayukan jama'a da dabobi da dama da ba za a iya kiyastawa ba, kuma an kasa yin noma a wasu wurare tsawon shekara uku saboda wannan matsala

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu rikicin dai a jihar Zamfara sun amince su mika makamai bayan cimma yarjejeniya da gwamnati

Baya ga fashin shanun dai, maharan kan dabbobi kama daga rakuma, da ƙananan dabbobi, har da dawakai da jakuna da akan ƙwace a hannun jama'a.

Akwai lokacin da aka kashe fiye da mutum talatin a lokaci guda, haka kuma a wurare daban-daban an kashe sama da mutum dari cikin jihar a rana ɗaya.

Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Zamfara inda aka kaddamar da atisayen sojoji don yakar 'yan fashin shanun, sai dai hakan bai yi wani tasiri ba sai da aka nemi sasantawa da maharan.

Ana ganin matakin da hukumomin jihar suka dauka na ɓullo da shirin raba masu rikicin da makamai a watan Fabrairu ya fara tasiri sosai, bayan cimma yarjejeniya sulhu.

Labarai masu alaka