'Idan kana son shaidar digirinmu sai ka iya ninkaya'

Swimmer Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Sabuwar dokar ta jami'ar Tsinghua ta janyo muhawara mai zafi birnin Beijing

Ɗaya daga cikin shahararrun jami'o'in China, Tsinghua ta faɗa wa ɗalibanta cewa sai sun iya ninƙaya kafin su samu shaidar kammala karatun digirin jami'ar.

Tsinghua wadda ake kira Harvard ta Gabas, ta tsai da shawarar cewa dole sai manyan haziƙan ƙasar sun yi zarra a fagen ninƙaya.

Labarin dai ya watsu a shafukan sada zumunta na China, har ma wasu na tuhumar ma'anar wannan mataki a ƙasar da ke fama da fari.

Sai dai, jami'ar ta kare matakin da cewa, ai kuwa ninƙaya muhimmiyar ƙwarewa ce da za ta bai wa mutum damar tsira.

Shugaban jami'ar Tsinghua, Qiu Yong ya ce motsa jini ta hanyar ninƙaya ya zama jazaman ga duk ɗalibai saboda yana inganta ƙoshin lafiya.

Tun a 1919 ne ɗaya daga cikin jami'o'in China da ake martabawa, Tsinghua ta fara neman ɗalibai su iya ninƙaya, amma daga baya ta watsar saboda shahararta da kuma rashin kududdufan ninƙaya a Beijing.

Sai dai, a ƙarƙashin sabuwar dokar da jami'ar ta sanar ranar Litinin, sabbin ɗaliban da za su fara karatu a watan Satumba sai sun buga nutso don nuna cewa za su iya ninƙaya tsawon aƙalla mita hamsin da kowanne irin salo.

'Dokokin kama-karya'

Sanarwar ta haifar da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta inda wasu ke tambayar azancin tunanin mutanen da suka tashi a tsandauri a ce sai sun koyi ninƙaya.

Wani Yixunsangyao ya rubuta cewa "Me zai faru ga ɗaliban da suka fito daga wuraren da ba su da ruwa ko kogi fa?"

Wani kuma Xishuoge ya rubuta: "ko da yake, fitacciyar jami'a ce, duk da haka bai kamata ta rika ɓullo da dokoki kara zube ba, don kuwa irin waɗannan dokoki ka iya dakushe baiwar mutum.

Wasu kuma kamar Shin-ssi, sun yaba wa jami'ar a kokarinta na bunƙasa wata "ƙwarewa da za ta taimaka wajen kuƙutar da rai".

Labarai masu alaka