Cristiano Ronaldo ya zama mai dogon zamani

Madeira Airport
Image caption Tun a farkon wannan mako ne aka kafa hoton Cristiano Ronaldo a jikin ginin filin jirgin Madeira

A wata karramawa da ba kowanne fitaccen ɗan ƙwallon ƙafa ke samun irinta ba, a Larabar nan ce za a yi bikin sanya wa wani filin jirgin sama sunan ɗan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo.

Ɗan wasan dai ya lashe gasar zakarun Turai, kuma ya ɗauki gwarzon ɗan ƙwallo na duniya wato Ballon D'or sau huɗu, ya ci kofunan gasar Turai a Manchester United da Real Madrid.

Baya ga cin kofin gasar ƙwallon ƙafa a Portugal da ɗumbin kyautuka a gasar Firimiyar Ingila da La Liga ta Spaniya, a yanzu filin jirgin sama sukutum za a sanya wa sunansa.

Ana sa ran Ronaldo zai halarci bikin sauya sunan filin jirgin a mahaifarsa da ke tsibirin Madeira. wanda za a maye da Cristiano Ronaldo.

Tun da ma an yi mutum-mutuminsa na azurfa a Madeira, an kuma sanya wa wani gidan adana kayan tarihi da otel laƙabinsa na CR7 moniker.

Ba Ronaldo ne ɗan ƙwallon ƙafa a duniya da ya fara samun wannan tagomashi ba, don kuwa Belfast ta yi wa marigayi George Best irin wannan karramamawa.

Amma dai ba ƙaramar ɗaukaka ba ce a rayuwa. Filin jirgin sama sukutum, ko babban abokin gasar shi Lionel Messi bai samu haka ba.