Nigeria: Buhari zai nada sabbin ministoci

Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana rade-radin cewar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai yi garambawul a majalisar zartarwar kasar

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya gabatar da sunayen mutum biyu wadanda yake son nada wa a matsayin ministoci ga majalisar dattawan kasar.

A wata wasikar da shugaban ya aika wa majalisar, wadda shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya karanta a ranar Laraba, shugaba Buhari ya gabatar da sunan Suleiman Hassan daga jihar Gombe da kuma Farfesa Stephen Ocheni daga jihar Kogi.

Mutanen biyu za su maye gurbin tsohon karamin ministan kwadagon kasar, marigayi James Ocholi, da tsohuwar ministar muhalli ta kasar, Amina Mohammed.

James Ocholi ya rasu ne a wani hatsarin mota a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2016.

Ita kuma Amina Mohammed ta yi murabus a matsayin ministar kasar ce ranar 24 ga watan Fabrairu, sakamakon nada ta mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya, aikin da ta kama a watan Maris na shekarar 2017.

A yanzu dai a iya cewa za a zuba ido ne don ganin ko 'yan majalisar za su amince da tabbatar da sunayen wadanda aka gabatar din ko za su yi fatali da su, sakamakon takun sakar da ya bullo na baya-bayan nan tsakanin bangaren zartarwar kasar da majalisar.

A ranar Talata ne majalisar dattawan Najeriya ta ki tantance wasu kwamishinonin hukumar zaben kasar da shugaba Buharin yake son nadawa, don nuna adawa kan yadda bangaren zartarwar ya bar mukaddashin shugaban EFCC ya ci gaba da jagorantar hukumar, duk da yake majalisar ba ta tabbatar masa da mukaminsa.

Wannan al'amari dai yana son jawo zaman doya da manja sosai a tsakanin bangarorin biyu.

Labarai masu alaka