Kalubalen da za mu samu da EU — Birtaniya

Birtaniya ta shafe shekaru 44 a cikin kungiyar Tarayyar Turai EU
Image caption Birtaniya ta shafe shekaru 44 a cikin kungiyar Tarayyar Turai EU

Firayim Ministan Biritaniya Theresa May, ta shaida wa BBC cewa,kasar za ta cigaba da cin moriyar kasuwanci tsakanin ta da kungiyar tarayyar turai, ko da bayan ficewarta daga kungiyar.

Da take magana jim kadan bayan Biritaniya ta sanar da aniyarta ta ficewa daga EU a hukumance, Misis May, ta ce kasar na bukatar a samu hadin kai wajen cimma yarjejeniyar da za ta bai wa Biritaniya damar cigaba da hada-hada a kasuwar bai-daya ta Turai.

A wata wasika da ta rubuta wadda ta kawo karshen zaman shekaru 44 da Biritaniya ta yi a cikin kungiyar,Misis May ta jaddada al'adarsu da ta zo daya da kasashen da ke cikin Eu, inda ta ce ta na fata za su cigaba da cin moriyar kawance da makwabtaka da juna.

Firayim Ministar, ta ce Biritaniya na fatan ci gaba da cin moriyar dangantaka da makwabtaka tsakanin ta da kungiyar ta EU.

Misis May ta ce za su fuskanci kalubale wajen cimma wata yarjejeniya mai dorewa tsakanin Biritaniya da EU, cikin shekaru biyu masu zuwa, amma tana da yakinin cewa hakan ya zama dole domin samun daidaito wajen amincewa da tsarin kulla dangantaka mai dorewa da kuma tsarin ficewar ta.

Labarai masu alaka