BBC Hausa na biki kan cika shekaru 60

Image caption BBC Hausa

A ci gaba da bukukuwan cikar BBC Hausa shekara 60 da fara watsa shirye-shiryen BBC Hausa, yanzu haka kafar tana gudanar da wani babban taro a Abuja, babban birnin Najeriya.

Manufar taron ita ce duba muhimmancin kafafen yada labarai wajen ci gaban al'umma, tare da bayar da shawarori kan yadda za a tunkari kalubalen da kafafen watsa labarai ke fuskanta.

Cikin wadanda suka halarci taron har da gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje, da kuma kakakin majalisar wakilan Najeriya, Mista Yakubu Dogara.

Babban mai gabatar da makala a wurin shi ne Farfesa Abdalla Uba Adamu na jami'ar Bayero dake kano.

Domin kallon abubuwan dake wakana a wurin taron, ku ziyarci shafinmu na BBC Hausa Facebook

Gabanin bude wannan taro, a wani sako na taya BBC Hausa murna, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya shafe shekaru yana sauraron BBC Hausa.

Ga abin da yake cewa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Shugaba Buhari na Najeriya