Yadda BBC Hausa ta yi shagalin cika shekara 60 da soma shirye-shirye

Sashen Hausa na BBC ya yi gagarumin biki na cikarsa shekara 60 da soma watsa shirye-shirye ga kasashen duniya. Bikin, wanda aka gudanar a Cibiyar tunawa da marigayi Shehu musa 'Yar Adua da ke Abuja, Najeriya, ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da 'yan jarida, ciki har da tsofaffin ma'aikatan BBC Hausa.