'Ba mu yarda da zaman 'yan Nigeria alkalai a Gambia ba'

Tun ba yau ba Gambia ke nada 'yan wasu kasashe a matsayin alkalai
Image caption Tun ba yau ba Gambia ke nada 'yan wasu kasashe a matsayin alkalai

Kungiyar lauyoyi a Gambia ta ce za ta shigar da kara kotu domin kalubalantar nadin da aka yiwa wasu 'yan Najeriya hudu a matsayin alkalan kotun koli a kasar.

A makon da ya gabata ne, gwamnatin kasar ta sake sabunta kwantiragin alkalan hudu, wadanda suka yi aiki a karkashin mulkin shugaba Yahya Jammeh.

Kasar Gambia dai na amfani da 'yan wasu kasashe a bangaren shari'a, saboda rashin kwararru 'yan kasar a bangaren.

To sai dai kuma, 'yan adawa a lokacin mulkin Mr Jammeh, na zarginsa da nada alkalai 'yan wata kasar ne saboda a cewarsu zai iya juyasu.

Labarai masu alaka