S/Africa: An sallami ministan kudi daga aiki

Ana matukar girmama Mr Parvin Gordhan a Afirka ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana matukar girmama Mr Parvin Gordhan a Afirka ta Kudu

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya kori ministan kudin kasar wanda ake matukar ganin kimarsa Pravin Gordhan, bayan wata jita jita da a ka rinka yadawa kwana da kwanaki lamarin da ya kawo rashin tabbas a kasuwar shunkun kasar.

A cikin wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar, ta ce an maye gurbinsa da ministan harkokin cikin gida Malusi Gigaba.

Ya zuwa yanzu dai an sallami ministoci goma sha biyar ke nan a kasar.

A farkon makon nan ne aka umarci Mr Gordhan da ya koma gida daga ziyarar da ya kai London, inda rahotannin suka nuna cewa shugaban kasar ya yi amanna ya je can ne domin ganawa da mutanen da ke shirya yi masa juyin mulki.

Tuni dai darajar kudin kasar ta fadi da kaso hudu cikin dari, saboda korar ministan da aka yi

Manyan masu fada aji na jam'iyyar ANC sun soki matakin korar Gordhan.

Labarai masu alaka