An cinna wa ginin majalisar dokokin Paraguay wuta

An tarwatsa masu zanga-zangar da harsashen roba da kuma ruwan zafi Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An tarwatsa masu zanga-zangar da harsashen roba da kuma ruwan zafi

Masu zanga-zanga a kasar Paraguay sun cinna wa majalisar dokokin kasar wuta a wani mataki na nuna kin jinin wani kudirin doka da zai sake bai wa shugaban kasar tsayawa takara a karo na biyu.

Hotunan da aka dauka sun nuna cincirindon masu zanga-zangar na barnata ginin majalisar, a daren Juma'a.

Cincirindon masu zanga-zangar dai ya yi wa ginin majalisar dokokin kawanya, a inda kuma suka fara huce takaicinsu da babballa tagogin zauren da shingen da ya zagaye ginin, kafin daga bisani su cinna masa wuta.

An dai ce masu zanga-zangar sun tsallaka cikin ginin majalisar a inda kuma suka nemi ofisoshin 'yan majalisar da ke goyon bayan kudirin dokar sannan suka banka musu wutar.

Tuni dai 'yan sandan kwantar da tarzoma suka tarwatsa dandazon jama'ar.

Daman dai mutanen sai da suka hau kan titunan kasar domin yin Allah-wadai da tattaunawar da 'yan majalisar dattawa suka yi a asirce kan kudirin da ke son yi wa tsarin mulkin kasar garanbawul.

Bisa al'ada, kafin kudurin ya zama doka, sai zauren majalisar wakilai ya sa masa albarka, wani wuri da jam'iyyar shugaban ke da gagarimin rinjaye.

Kundin tsarin mulkin Paraguay na 1992, ya takaita wa shugaban kasar damar sake tsayawa takara, a inda ya ba wa kowane shugaba wa'adin shekara biyar na karo daya.

To amma shugaban kasar mai ci, Oracio Cartes ya ga beken wannan tanadi a inda ya nemi ya yi masa 'yar kwaskwarimar da za ta ba shi damar sake cin gajiyar wani wa'adin.