An sace kwamfutocin jaridar Observer a Uganda

Uganda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani wurin sayar da jarida a Uganda

Barayi sun balle ofisoshin wani gidan jarida mai zaman kanta a Uganda, tare da sace akasarin kwamfutocin gidan jaridar.

Wannan ne karo na biyu cikin watanni shida da ake yi wa gidan jaridar ta The Observer irin wannan sata.

Jaridar wacce ofishin na ta ke Kampala, babban birnin kasar, tayi fice wajen binciken kwakwaf, kuma a lokuta da dama, gwamnati ta yi ta sukar ta.

Editan jaridar, Richard Kavuma, ya bayyana satar da aka musu a matsayin hari kan kafafen yada labarai masu zaman kansu a Uganda.