Harin bom ya jikkata 'yan sanda 16 a Masar

Egypt Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan sandan Masar yayin da suke sintiri

Wani bom ya tashi a Masar, inda ya jikkata mutane goma sha shida, kusan dukkan su 'yan sanda.

An dasa bom din ne a jikin wani babur da aka ajiye a wajen wata cibiyar horas da 'yan sanda a birnin Delta.

Wasu daga cikin mutanen da suka jikkata suna kwance a asibiti cikin mummunan yanayi.

Masu tayar da kayar baya a Masar sun yi ta kai hare-hare kan sojoji da 'yan sanda, tun bayan da sojoji suka hambarar da shugaban Mohammed Morsi a 2013.