Zaftarewar kasa ta kashe mutum 254 a Colombia

Columbia na fuskantar ruwan sama mai tsanani a wannan daminar
Image caption Rashin kyawun yanayi na tarnaki ga ayyukan ceto

Akalla mutane 250 ne ake tsammanin sun mutu sannan wasu 400 sun jikkata sakamakon ruftawar kasa a kasar Columbia, bayan tafka ruwa kamar da bakin kwarya a ranar Juma'a.

Har yanzu kuma ma'aikatan ceto fiye da dubu daya na ta neman mutane kimanin 200 da ake tsammanin suna karkashin laka.

To sai dai kuma rashin kyawun yanayi na tarnaki ga ayyukan ceton.

Daman dai shugaban kasar Juan Manual Santos, a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido ya ce akwai yiwuwar a samu karin mutanen da suka mutu bisa la'akari da girman bala'in.

Wani babban jami'in soji ya ce asibitin da ke birnin na Mocoa, na neman kasawa saboda yawan mutane.

An dai ce al'amarin ya faru ne sakamakon batsewar da tekun garin na Mocoa ya yi, a inda ya yi hankoro yana ambaliya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images/Colombia Army
Image caption Masu aikin ceto na ci gaba da lalubo mutanen da laka ta birne