'Da 'yan Niger cikin 'yan taddar da ke yakar jamhuriyar'

Jamhuriyar Nijar na fama da hare-haren ta'addanci
Image caption Jamhuriyar Nijar na fama da hare-haren ta'addanci

Babban jami'in kula da hukumar zaman lafiya ta jamhuriyar Niger, Kanar Abu Tarka ya ce akwai sa hannun 'yan kasar wajen kai mata hare-hare da kungiyar 'yan ta'adda ta Mali wato Mujao ke kai wa jamhuriyar.

Ya ce da wasu 'yan Niger da suka tsallaka Mali ake kitsa hare-haren.

Yankin Tillaberi dai na fuskantar hare-haren ta'addanci daga kungiyar ta Mujao, al'amarin da ya sanya gwamnati ta ayyana dokar ta-baci har na tsawon watanni uku.

Tuni dai hukumomin kasar suka yi kira ga mazauna yankin Tillaberi da ke iyaka da kasar Mali da su bai wa jami'an tsaro hadin-kai ta hanyar sanar da su duk wata bakuwar fuska da suka gani.

Hukumomin sun ce nuna bakin fuskokin, zai taimaka wajen yaki da ta'adancin da kasar ta sa a gabanta.

Gwamnan jihar Tillaberi, Ibrahim Kachalla wanda ya yi wannan kira, ya ce yankin na fama da hare-haren sari-ka-noke daga 'yantawaye na kasar Mali.

Jamhuriyar Niger dai na tsaka mai wuya sakamakon hare-hare daga kasashe masu makwabtaka da ita.

Kungiyar Boko Haram daga Najeriya da kuma Mujao da ke Mali na kai wa jamhuriya munanan hare-hare da ke sanadiyyar mutuwar mutane da jami'an tsaron kasar.

Labarai masu alaka