Paraguay: An kori minista daga aiki

Shugaba Cartes na son tsayawa takara ne a karo na biyu
Image caption Shugaba Cartes na son tsayawa takara ne a karo na biyu

Shugaban kasar Paraguay, Horacio Cartes ya kori ministan cikin gida da kuma shugaban 'yan sandan kasar bayan zanga-zangar da aka yi a ranar Jumma'a a kan yunkurin ba wa shugaban kasar damar sake tsayawa takara a karo na biyu.

Masu zanga-zangar dai sun yi ta jefan majalisar dokokin kasar, sannan kuma daga bisani suka cinna mata wuta.

Tuni dai mahukuntan kasar suka kama wasu jami'an 'yan sanda 4, bayan an kashe daya daga cikin masu zanga-zangar.

Shugabannin siyasa a kasar sun yi alawadai da kisan mutumin, inda suka yi kira da a gudanar da bincike a kan kisan.

Kundin tsarin mulkin Paraguay na 1992, ya takaita wa shugaban kasar damar sake tsayawa takara, a inda ya ba wa kowane shugaba wa'adin shekara biyar na karo daya.

To amma shugaban kasar mai ci, Horacio Cartes ya ga beken wannan tanadi a inda ya nemi ya yi masa 'yar kwaskwarimar da za ta ba shi damar sake cin gajiyar wani wa'adin.

Bisa al'ada, kafin kudurin ya zama doka, sai zauren majalisar wakilai ya sa masa albarka, wani wuri da jam'iyyar shugaban ke da gagarimin rinjaye.