'Shekara 50 ina sauraron sashen Hausa na BBC'

Muhammad Bashir Abubakar
Image caption Bashir Abubakar ya ce BBC shakundum ce

Wani mutum wanda ya ce ya kwashe shekara 50 yana sauraron sashen Hausa na BBC, ya ce a sashen ya fara jin labarin juyin mulkin da aka yi wa Sardauna, Sir Ahmadu Bello.

Malam Muhammad Bashir Abubakar ya yi takanas tun daga garin Mubi na jihar Adamawar najeriya zuwa ofishin BBCn da ke Abuja.

Malam Bashir ya kwatanta sashen Hausa na BBC da makaranta, a inda kuma ya rera wa kafar watsa labaran waka.

Sai dai kuma Malam Bashir ya ce abun da ya kamata sashen ya lura da shi a nan gaba shi ne fassara wa masu saurare abun da wasu 'yan Boko ko kuma wadanda ba su iya Hausa ba sosai.

Ya ce idan ana hira da irin wadannan mutane suna gwama turanci ko Faransanci da Hausa.

Ku saurari tattaunawar Malam Bashir Abubakar da Yusuf Tijjani a filinmu na Taba Kidi Taba Karatu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Muhammad Bashir Abubakar