Kotu ta ce a bai wa Saudiyya tsibirai a Bahar Maliya

Egypt Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kebe tsibiran Tiran da Sanafir domin girke dakaru musanman masu wanzar da zaman lafiya

Wata kotu a Masar ta ce shawarar da aka yanke ta hana mika wasu tsibirai biyu dake Bahar Maliya ga kasar Saudiyya, shawara ce da ba ta halasta ba.

Akwai yiwuwar wannan hukuncin kotun ya dawo da takaddamar da ta barke a bara, lokacin da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya ce za a mika wa Saudiyya tsibiran biyu da babu mutanen dake rayuwa a cikinsu.

A watan Janairu ne wata kotu ta yi watsi da yunkurin na shugaba Sisi.

Sai dai akwai yiwuwar a kara daukaka kara a kan wannan hukuncin na baya-bayan nan, sannan dole a karshe, sai majalisar dokokin Masar ta amince kafin a mika tsibiran ga Saudiyya.

Dangantaka tsakanin Masar da Saudiyya ta dan gyaru a baya-bayan nan, inda har shugaba Sisi ya amince ta gayyatar da aka mushi ta kai ziyara Saudiyya a wannan watan.