Ba zan gyara kundin tsarin mulki ba don 'tazarce'— Issoufou

Mahamadou Issoufou Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou

Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ya ce ba zai yi wa kundin tsarin mulki na kasar gyaran fuska ba domin ya bashi damar sake neman shugabancin kasar a karo na uku bayan cikar wa'adin shugabancinsa a 2021.

Kudin tsarin mulkin Nijar din ya tanadi wa'adi biyu ne na shekara biyar-biyar ga shugaban kasar.

A jawabin da ya yi wa jama'a na cika shekara guda da da sake rantsar da shi a matsayin shugaban kasar karo na biyu, shugaba Issoufou ya ce babban burin shi, shi ne ya shirya zabe na gaskiya a 2021, sannan ya mika mulki ga mutumin da 'yan kasar za su sake zaba a lokacin.

Shugaba Mahamadou Issoufou ya ce "ni dan siyasa ne, kuma ba na jin cewa ba za a samu kamata wanda zai maye gurbi na ba".

A cewar shugaban, Nijar na bukatar samun karfafan turakun dimukradiyya, kuma a saboda haka ne ake bukatar samun sauyin shugabanni.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A 2016 ne aka sake zaban Mahamadou Issoufou a karo na biyu

Masu sharhi dai na ganin, idan shugaba Mahamadou Issoufou ya cimma wannan buri na shi, zai zama zababben shugaba na farko a kasar da ya tabbatar da mika mulki cikin lumana ga wani sabon shugaban.

A shekarar 2010 ne aka hambarar da magabacinsa, Mamadou Tandja a wani juyin mulki, sakamakon yunkurinsa na yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, don ya bashi damar ci gaba da zama a mulki bayan cikar wa'adin shugabancinsa biyu.

Masu sharhi na cewa tun bayan samun 'yan cin kai a 1960, ba a taba samun wani lokaci da zababben shugaba ya mika mulki cikin ruwan sanyi ga wani zababben shugaban a Nijar ba.

A shekarar 1993 kasar ta koma tafarkin dimukradiyya, amma ta yi ta fama da matsalar juyin mulki daga sojoji.