Mai hidima a wurin ibada ya kashe mutane 20 a Pakistan

pakistan Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Wasu daga cikin wadanda suka jikkata a lamarin kwance a asibiti

Babban ministan lardin Punjab a Pakistan ya yi kiran a gudanar da cikakken bincike game da kisan akalla mutane ashirin da wani mai hidima a wurin ibadar Sufaye ya yi.

Rahotanni sun ce Abdul Waheed ya kira mutanen zuwa cikin dakin shi daya bayan daya, inda ya sassara su da adda.

Wani jami'in dan sanda ya ce mutumin mai shekaru hamsin, wanda ya amsa cewa ya aikata laifin, yana da alamu na tabin kwakwalwa.

Rahotanni sun ce mutumin ya shaida wa 'yan sanda cewa mutanen da ya kashe din, sun yi yunkurin kashe shi ne shi ma.

Lamarin wanda ya auku a kusa da birnin Sargodha, ya girgiza mutanen yankin sosai.