An yi bukin baje kolin fina-finai a Saudiyya

saudi festival Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lokacin wani bikin baje kolin fina finai a birnin Dammam City a watan Maris 2017

Wani fim da aka shirya kan tsattsaurar akida ta addini, ya lashe babbar kyautar da aka sa a bukin baje kolin fina-finai a Saudiyya, kasar da aka haramta cinima.

Fim din mai suna Departures, ya bayar da labarin wasu fasinjoji biyu ne a jirgin sama, wadanda dukkan su ke da burin kashe kansu, daya da sunan jihadi, dayan kuma saboda yana fama da wata cuta da ba a warkewa.

Wannan ne karo na hudu da ake gudanar da bikin baje kolin fina-finai a Saudiyya, wani abu da ke alamta samun sauyi da kadan-kadan na amincewa da nishadi a bainar jama'a a kasar.

Wata hukuma ta gwamnati da aka kafa a 2016 don kula da baje kolin, ta bayyana wannan shekarar a matsayin shekarar nishadi a Saudiyya.