'Jama'a ne za su yanke hukuncin ƙarshe kan dokar aure'

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II
Image caption Kabiru Alhassa Rurum ya ce da majalisar dokoki da masarautar Kano duk jama'a suke wakilta

Majalisar dokokin jihar Kano a Najeriya ta ce jama'ar jihar ne za su yanke hukuncin ƙarshe a kan ƙudurin dokar hana talaka futuk auren mace fiye da ɗaya.

Majalisar ta ce sai ta gudanar da zaman sauraron ra'ayin jama'a don jin ko ƙudurin dokar auren ta dace da muradin al'ummar jihar, da zarar an gabatar mata da kundin.

Shugaban majalisar, Hon. Kabiru Alhassan Rurum yayin wata tattaunawa da BBC ya ce, da ma daɗin dimokraɗiyya kenan, don haka majalisa za ta bai wa malamai da sarakuna har ma da sauran jama'ar gari damar bayyana ra'ayoyinsu a kan ƙudurin dokar.

Ƙudurin dokar auren wadda sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II ke son ɓullo da ita na ci gaba da janyo taƙaddama mai zafi a ciki da wajen Kano.

Kudirin dai ya ƙunshi batutuwan auratayya iri daban-daban waɗanda sarki Sanusi ke ganin sun janyo taɓarɓarewar harkokin zamantakewa da tarbiyya.

Kabiru Rurum ya ce: "Kamar yadda al'adar gabatar da dokoki take, za a yi wa (ƙudurin) dokar karatu na ɗaya da na biyu. Kuma haƙiƙa, na tabbatar da cewa za mu bai wa al'umma dama musammam malamai da sarakuna da su kansu ma'auratan."

"A zo a yi taro na jin ra'ayin al'umma a ga shin wannan doka ta yi daidai da abubuwan da addinin musuluncinmu ya tanada ko kuwa akwai wani abu da ake ganin ya kamata a gyara a ciki."

A cewarsa: "Fadar sarkin Kano ita ma al'umma suke mulka kuma su suke wakilta, wanda na tabbatar da cewa ra'ayin jama'a shi ne a gabansu..."

"Na tabbatar a ƙarshe dukkan abin da al'ummar Kano suka ga ya fi dacewa a kan wannan doka. Idan aka yi shi ita ma fada za ta goyi baya ko da ya yi daidai da ra'ayinta ko bai yi daidai da ra'ayinta ba."

Labarai masu alaka