Nigeria ka iya zuwa gasar tseren motar ƙanƙara ta Olympics

Nigerian Bobsleigh
Image caption Ayarin shi ne na farko da zai wakilci nahiyar Afirka a gasar tseren motar ƙanƙara, matuƙar ya samu cancanta.

Wasu tsoffin 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle uku da suka fito daga Nijeriya, na can suna atisaye don wakiltar Nijeriya a wasan tseren motar ƙanƙara na gasar Olympics da za a yi cikin Koriya ta Kudu a baɗi.

Babu dusar ƙanƙara a ƙasashen Afirka ta yamma kamar Nijeriya, don haka ne 'yan wasan suka niƙi gari daga Amurka zuwa Calgary a can yammacin kasar Canada domin atisaye.

Hakan dai na nuna cewa 'yan wasan sun bi sahun wani ɗan wasan Jamaica wanda a 1988 ya nema wa kasarsa suna a wasan zamiyar ƙanƙara.

Wata 'yar Nijeriya, Seun Adigun ce ta ɗauki gabarar horas da 'yan wasan tseren motar ƙanƙarar na Nijeriya bayan ta lura cewa ƙasarta ba ta samun wakilci a irin wannan wasa yayin gasar Olympic.

Image caption A yanzu haka suna ƙasar Kanada inda suke atisaye

Seun Adigun tsohuwar 'yar wasan tseren ƙanƙara ce da ke zaune a birnin Houston na Amurka, don haka take amfani da basira da ƙwarewar da Allah ya ba ta wajen horas da wasu mata 'yan Nijeriya Ngozi Onwumere da Akuoma Omeoga ta yadda za su iya wakiltar Nijeriya a Olympic.

Kafin Nijeriya ta iya shiga wasan, sai ƙungiyar ta yi atisaye biyar a cikin ƙasa uku, kuma ya zuwa yanzu 'yan wasan sun yi nasarar zuwa ƙasa biyu.

Sai dai har yanzu ƙungiyar ba ta samu wani abin a-zo-a-gani ba a gidauniyar da ta kafa don tara kuɗin da take buƙata dala dubu 150 da za ta ɗauki nauyin kanta a gasar wadda za a buɗe cikin watan Oktoban 2018.

Direbar ƙungiyar Seun Adigun da Ngozi Onwumere da kuma Akuoma Omeoga dukkansu tsoffin 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle ne.

Image caption Seun Adigun 'Yar Nijeriya ce mazauniyar Amurka kuma ta duƙufa wajen cim ma burin ɗaga tutar Nijeriya a gasar tseren motar ƙanƙanra

Babu wani ayarin 'yan wasan motar tseren ƙanƙara daga Nijeriya ko daga wata ƙasa a Afirka da ya taɓa wakiltar nahiyar a gasar Olympics.

Burin ƙungiyar dai ya kusa cika, don kuwa a yanzu suna buƙatar yin ƙarin wasa uku ne kafin su samu cancantar zuwa gasar Olympics ta 2018.

Labarai masu alaka