Nigeria: Kungiyar masu dakon mai ta dakatar da yajin aiki

Tankar man fetur mallakin kamfanin man Najeriya, NNPC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar NUPENG ta ce ta janye yajin aiki

Kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur NUPENG, ta janye yajin aikin da ta soma kasa da sa'a 24 da kaddamarwa.

A ranar Litinin ne kungiyar direbobin manyan motocin dakon man fetur ta so ta fara yajin aiki a Najeriya.

Shugaban na NUPENG, Igwe Achese, ya shaida wa BBC cewa kungiyar ta janye yajin aikin, bayan da kamfanin mai na kasa NNPC ya sanya baki a rikicin.

Tun da farkon taron da aka gudanar kan shawo kan lamarin, Daraktan kamfanin NNPC Maikanti Baru, ya yabawa Mista Achese da kokarin da ya yi wajen ganin an shawo kan matsalar.

Kazalika ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta amince da karin kashi 16.3 cikin dari a kudin alawus-alawus din da ake biyan dilallan man fetur din.

Kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas ta NUPENG ta ce za ta shiga yajin aikin ne saboda karancin albashi da lalatattun titunan kasar da suke bata musu motoci.

Labarai masu alaka