'Yadda 'yan Boko Haram suka hallaka mazajenmu'

Borno Maiduguri
Image caption Boko Haram ta bar mu da marayu

Hare-Haren Boko Haram musammam a Maiduguri babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya sun haifar da dubban marayu da kuma matan da aka kashe wa maza aka bar su da ɗawainiya.

Akwai ɗumbin mata da ƙananan yara musammam a Maiduguri, da ke cikin halin tagayyara sakamakon raba su da mazan da suka dogara da su wajen kula da rayuwarsu da ta 'ya'yansu.

Akasarin wadannan mata ba su da aikin yi, ko wata sana'a, lamarin da ke wasunsu yin barace-barace don neman abin da za su ciyar da kansu da 'ya'yansu.

Dubban irin wadannan mata da 'yan tada-ƙayar-baya suka kashe mazajensu na zaune a gidajen 'yan'uwa da abokan arziki, wasu kuma a gidajensu na gado, baya ga dandazon wasu da ke sansanonin gudun hijira.

Image caption Wasu daga cikin matan da ke sansanonin 'yan gudun hijira na yin wasu 'yan sana'oi

Bilkisu Babangida da ke cikin wani ayarin BBC da ya kai ziyara jihar Borno kwanan baya, ta yi tattaki zuwa unguwar Ngomari Costain a cikin birnin Maiduguri don ganin yadda waɗannan mata ke rayuwa.

Dukkansu labarin ɗaya ne -- 'yan Boko haram sun kashe musu mazaje -- ko da yake, kowacce na da bayani iri daban kan yadda wannan iftila'i ya same mata.

Malama Ya Mera wadda 'yan Boko Haram suka kashe maigidanta a cikin shekara ta 2011, ta ce rayuwar ba mai sauki ba ce a yanzu. Ta ce har ƙofar gida 'yan Boko Haram suka je suka kashe mijinta a lokacin.

''Ina zaune a cikin gida sai ya ce wa yarona ya kawo masa ruwan alwala, kafin ya kai masa sai kawai muka ji karar bindiga a waje, sai muka ji yana salati, sun harbe shi, kafin a karasa da shi asibiti ya rasu.''

Ta kuma ce yanzu haka ta shiga halin kunci saboda dawainiyar yara goma da aka bar mata, duk da dai tana dan samun taimako daga 'yan uwa, tana kuma sayar da gawayi da itace.

Image caption Matan da dama suna cikin halin kunci tun bayan da 'yan Boko Haram suka kashe mazajensu

Ita kuwa Malama Fatima cewa ta yi ba za ta taɓa manta halin da ta samu kanta a ciki ba shekaru uku da suka gabata lokacin da yan Boko Haram suka hallaka mijinta gami da 'ya'yanta uku.

''Da karfe goma sha ɗaya na dare suka shiga gidanmu, suka yi sallama, a cikin gidan namu a daki daya, mutum hudu da maigidana da yaranmu uku duka suka kashe. Kin ga inda harsashi ya same ni a hannu''.

Malam Rukayya daga garin Gwoza a kudancin jihar Borno, ta ce 'yan tada-ƙayar-baya sun kashe maigidanta da yaronta saurayi lokacin tana da ciki wata biyu a yayin harin da suka kai garin.

'' Rayuwa dai ga ta nan muna lallabawa, yara guda takwas (aka bar min) wata ran akwai wata ran kuma babu, ina dai sana'ar tuyar waina da nake taimaka wa kaina da 'ya'yana''.

Rakiya Adam maigidanta malamin jami'a ne da shi ma ya gamu da ajalinsa a hannun Boko Haram a shekara ta 2012, ta ce sun kashe marigayin inda ya bar musu yara 13 ita da abokiyar zamanta.

"Ranar ya dawo daga aiki da yamma suna zaune a kofar gida da abokansa, bayan sun ci abinci sai wata mota ta zo ta haska su, sauran da ke zaune suka tsorata suka gudu, sai suka harbe shi, mun ji yana ta salati, da muka fito sai gawarsa muka gani a kofar gida.''

Image caption Boko Haram sun hallaka mijina da kanena

Fatima Ali kuma ta rasa maigidanta da ƙaninta ne lokaci guda a shekara ukun da ta gabata. ''Ina da tsohon ciki lokacin, da suka shiga ɗaki sai suka harbe maigidana da ƙanina, babana da yake taimaka min shi ma mako hudu kenan tun da ya tafi kasuwar Mainok ban sake jin labarinsa ba.''

Mijin Malama Zahra Adamu na cikin ɗakinsa yana barci shekaru hudu da suka wuce lokacin da 'yan Boko Haram suka shiga suka tashe shi bayan sun haura katangar gidan cikin tsakar dare inda suka fita da shi waje.

Ta ce "Da suka fita da shi waje, sai suka kulle mu ta baya, akwai yashi a kofar gidan a nan suka yanka shi."

Waɗannan mata da Boko Haram ta raba da mazajensu na cikin tsananin buƙatar abinci da kula da lafiya da kuma ilmi ga 'ya'yansu, baya ga tallafi don samun yadda za su iya tsayawa da kafafunsu.

Labarai masu alaka