Hari kan 'yan Nigeria a India 'nuna wariya ne'

Nigerians attacked in India Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kai hare-haren ne a yankin Greater Noida kusa da Delhi babban birnin ƙasar Indiya

Jakadun ƙasashen Afirka a Delhi babban birnin ƙasar Indiya sun yi Allah wadai da hare-haren da aka kai a baya-bayan nan kan ɗalibai 'yan Nijeriya a birnin.

A cikin wata sanarwa, jami'an diplomasiyyar na Afirka sun ce hare-haren nuna "ƙyamar baƙi ne da wariyar launin fata".

Jakadun sun kuma ce hukumomin Indiya sun gaza yin "gamsasshen Allah-wadai" kan hare-haren ko ɗaukar "matakan hana sake kai hare-haren a zahiri."

A cikin watan jiya ne aka far wa ɗaliban a yankin Greater Noida, kusa da birnin Delhi.

Image caption Endurance Amalawa ya ce yana tunanin Indiyawa sun tsani baƙaƙen fata

Wani cincirindon mutane ya far wa ɗalibai 'yan Nijeriya biyar, yayin da wasu suka yi wa wani ɗalibi a-ture a cikin wani babban kantin sayayya.

Mutuwar wani saurayi ba'indiye ce bayan ya yi mankas da kwaya ta janyo wannan tarzoma. Iyayensa dai sun zargi ɗalibai 'yan Nijeriya da ba shi ƙwaya.

Image caption Iyayen Ba'indiyen sun zargi ɗalibai 'yan Nijeriya da ba shi ƙwayar da ta zama ajalin rayuwarsa

'Yan sanda sun ce sun kama mutum biyar kan wannan tarzoma, yayin da ministar harkokin wajen Indiya Sushma Swaraj ta yi alƙawarin gudanar da bincike " tsakani da Allah".

Sai dai jakadun Afirkan sun ce hakan bai wadatar ba, inda suka bukaci kwamitin kare haƙƙin Ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ya binciki lamarin.

Sun kuma nemi "Gwamnatin Indiya a manyan matakai su yi Allah wadai cikin kakkausar murya, da kuma hanzarta gurfanar da masu hannu cikin lamarin a gaban shari'ah".

Wasu masu sayayya sun naɗi farmakin da aka kai wa wani ɗalibi a wani babban kanti da wayar salula har ma aka yaɗa bidiyon a kafofin sada zumunta.

Image caption Endurance Amalawa ya ce yanzu ya fasa ci gaba da yin digiri na biyu a India

Ɗalibin ya fada wa manema labaran Indiya cewa an doke shi da rodi da bulo kuma an caka masa wuƙa. Ya ce babu wanda ya ƙwace shi ko ya taimaka da kiran 'yan sanda.

Indiyawa da dama sun mayar da martani cikin jin kunya a shafukan sada zumunta. Ko da yake, akwai lokutan da 'yan Afirka mazauna Indiya a shekarun baya-bayan nan suka fuskanci wariya ko kuma cin zarafi.

An yi wa wani dan kasar Congo duka har ya ce ga garinkiu nan a watan Mayun 2016 a Delhi bayan gardama ta barke a kan babur mai ƙafa uku.

Wata uku kafin nan, cincirindon Indiyawa ya far wa wani ɗalibi ɗan ƙasar Tanzania har aka kusan yi masa zigidir a birnin Bangalore. A shekara ta 2013 ma, an daba wa wani dan Nijeriya wuƙar da ta yi sanadin mutuwarsa.

A lokaci guda kuma, 'yan sanda sun ce za a izo ƙeyar wata 'yar Kenya da ta yi ƙaryar an kai mata harin wariyar launin fata a Greater Noida.

Matar ta ce mutum biyar ne suka farɗo ta daga cikin wata motar taksi kwana biyu bayan harin da aka kai wa ɗalibai 'yan Nijeriya, sai dai 'yan sanda sun ce bincikensu ya nuna labarin ba haka yake ba.

Labarai masu alaka