Ƙwararru sun ƙirƙiro rariyar tace ruwan teku

Rariyar tace ruwan gishiri Hakkin mallakar hoto UNI MANCHESTER
Image caption Burin binciken shi ne ullo da wata hanyar tace ruwan sha daga ruwan gishiri na teku

Masana kimiyya a Burtaniya sun ƙIrƙiro wata rariya da za ta iya tace gishirin da ake samu a ruwan teku.

Wannan ci gaba da ake rububinsa ka iya bunƙasa hanyar samun tsaftataccen ruwan sha don miliyoyin al'ummar duniya.

Ta hanyar rariyar mai raga-ragar da za ta iya tace gishiri, masu binciken sun ce hanyar za ta fi waɗanda ake amfani da su yanzu wajen rairaye gishiri daga cikin ruwa.

A baya, abu ne mai wahala sarrafa wata raga irin wannan mai yawan da za a iya samarwa don amfanin masana'antu.

"Wakilin BBC ya ce sabon binciken ka iya rage tsadar raba gishiri da ruwan teku wadda masana'antu ke amfani da ita. Sai dai, akwai buƙatar sai masana ilmin kimiyyar sun ƙara inganta binciken kafin wannan rariya ta graphene ta iya fitowa daga ɗakunan bincike."

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Samun tsaftataccen ruwan famfo babban ƙalubale ne ga miliyoyin al'ummar duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi hasashen cewa nan da shekara takwas sama da kashi 14 cikin 100 na al'ummar duniya za su yi fama da ƙarancin ruwa.

Da suke gabatar da rahoton sakamakon binciken a mujallar Nature Nanotechnology, masana kimiyyar daga jami'ar Manchester, a ƙarƙashin jagorancin Dr Rahul Nair ya nuna yadda suka shawo kan wasu matsalolin tace ruwan gishiri ta wannan hanya.

Labarai masu alaka