Nigeria: Sakin tsohon gwamna ya sa an dakatar da gandurubobi

Ngelari
Image caption Mutane da dama sun yi mamaki kan yadda tsohon gwamnan ya yi saurin samun wannan beli 'yan kwanaki bayan kotu ta ɗaure shi

Kwamitin gudanarwa na hukumar gidajen yari a Najeriya ya dakatar da wasu manyan jami'an tsaron gidajen yari uku, saboda sakin wani tsohon gwamna daga kurkuku.

An samu jami'an da laifin haɗa baki wajen bayar da rahoton lafiya ba bisa ƙa'ida ba ga Bala James Nglari da ke zaman ɗaurin shekara biyar a gidan yarin Yola.

Jami'an sun hadar da CP Peter Yeni Tenkwa, da DCP Abubakar Abaka da kuma SP John Bukar.

A cikin wata sanarwa, wani daraktan kwamitin Mista Sunday Dan Ogu, ya ce an dakatar da jami'an ne sai an kammala dukkan bincike a kan batun.

Kawo yanzu babu tabbas kan abin da zai faru ga Mista Nglari.

Wata kotun ɗaukaka ƙara ce ta ba da belin ɗaurarren, bayan ya gabatar da mata da wata takarda da ta fito daga jami'an tsaron gidan Yola game da taɓarɓarewar lafiyarsa.

Takardar dai ta yi bayanin cewa tsohon gwamnan ba zai iya samun kulawar lafiya da yake buƙata a asibitin gidan yarin ba, don haka sai an kai shi babban asibiti.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon gwamna Ngelari a gaban kotu

Babbar kotun jihar ta yanke wa James Nglari ɗaurin shekara biyar a gidan yari saboda saba wa ƙa'idojin bayar da kwangila.

Alkalin kotun Nathan Musa ya samu tsohon gwamnan da aikata laifi hudu cikin biyar da aka tuhume shi.

Shi ne gwamna na biyu da aka taba daure wa kan zargin cin hanci da rashawa tun bayan komawar Najeriya tafarkin demokraɗiyya a 1999.

Shi dai Nglari ya ce bai amince da hukuncin ba, kuma zai ɗaukaka ƙara.

Labarai masu alaka