'Shugabanni ne suka jawo fushin Allah a Zamfara'

Yari Hakkin mallakar hoto PREMIUM TIMES
Image caption Abdul'aziz Yari ya ce laifin da ake yi wa Allah ne suka janyo sanƙarau

Al'ummar jihar Zamfara na ci gaba da mayar da martani kan furucin da gwamnan jihar Abdul'aziz Yari ya yi cewa saɓon Allah da ake yi ne ya janyo annobar sanƙarau da ake fama da ita a Nijeriya.

Gwamnan yana jawabi ne kan halin ake ciki sakamakon annobar sanƙarau da ta kashe sama da mutum 300 a jihohin da aka samu ɓullarta a Nijeriya.

Ya ce yana ganin sanƙarau ta sauya daga nau'in da aka santa a Nijeriya zuwa wani daban da ke tagayyara mutane ne saboda ƙaruwar aikata saɓo da al'umma ke yi.

Sai dai wasu 'yan jihar ta Zamfara sun bayyana rashin jin dadi a kan waɗannan kalamai da gwamnan ya yi, a daidai lokacin da mutane ke ci gaba da mutuwa sakamakon annobar.

Sama da mutum 200 ne a hukumance ya zuwa yanzu aka ba da rahoton cutar sanƙarau ta yi sanadin mutuwarsu a Zamfara kaɗai.

A wani jin ra'ayoyin jama'a da BBC ta tattara, wani mutumin jihar ya ce idan batu ne na saɓon Allah, to bai kamata gwamna Yari ya fitar da kansa ba, don kuwa kowa yana saɓon Allah.

"Ya ce saɓon Allah, talaka na yi, na ƙasa na yi. Su da ac ciki(n gwamnati) na yi."

A cewarsa akwai inda ake tafka saɓon Allah da ya fi na jihar Zamfara, amma Allah bai ƙaddara musu wannan annoba ba.

Shi ma wani mutumin jihar ya ce in dai aka ce Allah ne ya kawo annoba, ba shakka sun yarda da Allah, don haka suna roƙonsa ya kawo musu sauƙinta.

Shi kuma wani daban ya ce gaskiya maganar da gwamna (Yari) ya faɗa ba ta dace ba.

Ya ce matuƙar suna ganin saɓon Allah ne ya kawo annoɓar sanƙarau, to a gwamnati ake aikatawa.

"In fushin Allah ne (ya kawo annobar sanƙarau) to waye sanadi? Ai su ne sanadiyya. Su ne shugabanni su suka janyo."

Sai dai mashawarci na musamman ga gwamnan jihar Zamfara kan harkokin yaɗa labarai, Alhaji Ibrahim Dosara ya ce ba a bahaguwar fahimta aka yi wa kalaman da gwamna Yari.

Labarai masu alaka