An sako 'yan Nigeria da IS ta kama a Libya

'Yan kungiyar IS
Image caption Wasu daga cikin matan na kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai, lokacin da mayakan IS suka yi garkuwa da su

'Yan Najeriya bakwai na cikin mata 35 da mayakan IS suka kama a garin Sirte da ke ƙasar Libya, kuma suka mayar da su bayi da suke lalata da su har na tsawon watanni.

'Yan Najeriyar sun hada da yara biyu da 'yan kasar Eritreans 28 wadanda sojin kasar Libya suka gano a watan Disambar da ya gabata, sannan suka fuskanci wani hukuncin tsarewa a kurkukun garin Misrata. Sai dai yanzu haka mahukuntar kasar Libya sun sallame su.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mutanen sun tsere daga garin Sirte, wani tsohon wurin kungiyar IS da ke cikin tsakiyar kasar Libya, yayin da sojojin da ke kusa da birnin Misrata suka yi yaki don hambarar da 'yan tawayen a shekarar da ta gabata.

Wasu daga cikin matan na kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai, lokacin da mayakan IS suka yi garkuwa da su kuma suka tsaresu suna jima'i da su a matsayin bayi.

Daga nan sun tsere daga garin Sirte, sai aka ajiye su a kurkukun Misrata na tsawon watanni aka yi musu bincike a kan ko suna da alaka da kungiyar.

Kamfanin Reuters ya yi bayanin yadda IS suka yi amfani da bautar da 'yan gudun hijira mata wajen biyan mayakansu na kasar Libya.

A labaran da aka wallafa shekarar da ta gabata, matan sun kara bayyana yadda kungiyar ta tilasta musu shiga Musulunci da kuma sayar da su a matsayin bayi da za a rika jima'i da su.

A watan Nuwamba, wakilin kamfanin Reuters ya ziyarci wasu da aka kama a garin Misrata.

Daya daga cikin matar ta ce, sannan sababbin shugabanninsu suna azabtar da su da yunwa da kuma kaskantar da su. Akwai mace guda 'yar shekara 16 tana da ciki kuma tana bukatar kulawa ta gaggawa.

Image caption Kungiyar IS ta sha kama da tsare mutane tana bautar da su

Ofishin atoni janar na kasar Libya ya bayar da sanarwa cewa sun gana da matan da suke masha'ar a tsakiyar watan Fabrairu, sai dai an samu jinkiri wajen sallamarsu, ba tare da wani bayani ba.

A ranar Laraba, sun karbi bakuncin ma'aikata daga Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNHCR da kuma Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Libya kafin a kai su zuwa masauki don duba lafiyarsu.

Wata yarinya 'yar shekara 14, 'yar kasar Eritrean ta shaidawa Reuters cewa," na yi matukar farin ciki, ba zan iya bayyana yadda nake ji ba, amma na ji dadi, yanzu zan fara sabuwar rayuwa kuma na ga 'yan uwana". Ta fadi haka ne kafin fitowarsu kurkuku.

Hukumar na tsammanin kara ba wa 'yan kasar Eritreans wurin zama a matsayin 'yan gudun hijira.

Shugaban UNHCR na kasar Libiya, Samer Haddadin ya ce, "zamu tura su zuwa gida, inda za a kula da su idan suna bukatar magani, kuma za su samu taimako daga kasar Amurka da kuma kariya".

Ya ci gaba da cewa, a lokaci guda muna duba yadda zamu ba su kulawa a matsayin 'yan gudun hijira, kuma muna yin haka ne don mu tabbatar mun samu kasar da za ta bayar da matsugunni ga wadanda suka hadu da matsalar wurin zama.

"'Yan Najeriyan mata biyar da kuma yara biyu, za a tura su wurin masu neman mafaka ko a ba su damar komawa gida."

Da yawan mata da kananan yaran da suka tsere daga garin Sirte, ko wadanda sojin Libya suka daukesu har yanzu suna garin Misrata.Wanda suka hada da 'yan kasar Libya da Tunisiya, da 'yan kasashen Afirka da dama. A watan Fabrairu ma an 'yanto ma'aikatan jinya na kungiyar Filipino.

Kungiyar IS sun karbe iko a garin Sirte a farkon shekarar 2015, inda suka mayar da birnin da ke bakin teku cibiyarsu da yake wajen kasar Siriya da Iraki, kuma nan ne tashar da suke ajiye daruruwan mayakansu na wasu kasashe. Dakaru Misrata sun shafe a kalla watanni bakwai kafin su kara kwato birnin.

Labarai masu alaka