Nigeria: 'Dole a biya 'yan fansho hakkokinsu'

Image caption Majalisar wakilan Najeriya ta ce da damu matuka da rashin biyan 'yan fansho hakkokinsu

A Nageria, majalisar wakilan kasar ta bayyana damuwar ta dangane da rashin biyan 'yan Fansho hakkokin su a kan lokaci, lamarin da kan haddasa 'yan Fanshon shiga mawuyacin hali na rayuwa.

A kan haka ne Majalisar ta umurci bangaren zartarwa da ya gaggauta biyan daukacin basussukan da 'yan Fansho ke bin gwamnati.

Majalisar ta ce ta gayyaci ministar kudi, Kemi Adeosun da kuma ministan kasafin kudi ,Senata Udoma Udoma, bayan korafe-korafe da suka samu daga jama'a da dama.

Majalisar ta ce ta lura da cewa 'yan fanshon ba sa samun tanade-tanaden da gwamnatai ta musu bayan sun yi ritaya, kuma gashi sun bautawa gwamnatin, shi ya sa ma suka kira ministocin biyu dan jin dalilin da ya sa ake samun matsaloli wajen biyan 'yan fansho a kan lokaci.

To sai dai kuma, ana su bangaren, ministocin sun bayyanawa majalisar wakilan dalilin da ya sa ake samun matsaloli wajen biyan 'yan fasnho, inda suka ce rashin isassun kudade ne ke haddasa matsalar.

Ministocin sun ce ba mamaki ko a cikin kasafin kudi majalisar ba ta kasafta abinda ya dace a biya 'yan fanshon, kuma wani lokaci a kan samu tsaiko kafin a samu kudin da za a biya.

Majalisar dai ta shaida wa ministocin cewa, dole a dauki matakan da suka dace domin tabbatar da ana biyan 'yan fansho kudadensu a kan lokaci, ba tare da an bar su har sun shiga mawuyacin hali ba.

Labarai masu alaka