An kama matashiya da shirin kai hari a Denmark

Image caption Wannan lamari na wannan matashiya ya yi matukar tada hankalin shugaban kasar Lars Løkke Rasmussen

A yaune za a gurfanar da wata matashiya 'yar shekara 16 a Denmark bisa zarginta da shirin kai hare-hare a makarantu biyu, wadda guda in da ta ke karatu ne.

Ana kyautata tsammanin cewa ita ce mace ta farko da aka kama da sunan tuhuma a kan aikata ta'addanci a Denmark.

Masu shigar da kara sun ce ta kai matakin farko a shirye-shiryen da ta ke na kai hari kan wata makarantar Yahudawa da kuma inda ta ke karatu a Copenhagen.

Matashiyar dai ta hada bam da kanta in da ta na shirin gwada shi ne aka kama ta.

Rahotanni sun ce yarinyar ba ta jima da karbar addinin islama ba, kuma ta na cikin wata kungiya a kafar sadarwa da ke goyon bayan wata kungiya mai kaifin kishin islama da aka dakatar da ayyukanta a kasashe da dama amma banda Denmark wato Hizbut-Tahrir.

Labarai masu alaka