'Yan ƙunar baƙin wake sun kashe kansu a Maiduguri

Sojoji sun sha alwashin kawo karshen Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojoji sun sha alwashin kawo karshen Boko Haram

Wasu mata 'yan kunar bakin wake biyu da suka tashi bama-baman da ke jikinsu a birnin Maiduguri na jihar Bornon Najeriya sun kashe kansu.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce akalla mutum biyar ne suka jikkata bayan sun yi yunkurin hana matan kutsa kai cikin wani masallaci da asubahin ranar Asabar.

Rahotanni sun ce matan 'yan tsakanin shekara 10 zuwa 13 ne.

Kungiyar Boko Haram, wacce ke amfani da kananan mata wurin kai irin wadannan hare-hare, na ci gaba da fuskantar matsi daga wurin jami'an tsaro.

Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashi murkushe kungiyar, kuma masu sharhi a kan sha'anin tsaro sun ce sojojin na samun galaba sosai a kan mayakan na Boko Haram.

Labarai masu alaka