EFCC ta kama maƙudan kuɗi a Lagos

EFCC ta ce tana yin bincike domin gano mutumin da ya mallaki kudin Hakkin mallakar hoto Efcc
Image caption EFCC ta ce tana yin bincike domin gano mutumin da ya mallaki kudin

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC ta ce jami'anta sun sake kama makudan kudi a wani babban shago a birnin Ikko da ke kudu maso yammacin kasar.

Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ta ce jami'an nata sun gano N448,850,000 a yashe a cikin shagon ne, wanda aka dade ba a bude shi ba, bayan an tsegunta mata cewa ana shirin canza kudin zuwa kudin kasashen waje.

A cewar EFCC, shagon na da tambarin masu canjin kudin kasashen waje, amma an kwashe sama da shekara biyu ba a bude shi ba.

Sanarwar ta ce, "Bayan mun samu labarin abin da ke faruwa ne sai jami'anmu suka je babban kantin da shagunan ke ciki, inda suka nemi sanin masu shaguna masu lamba SL 64 da SL 67. Da muka nemi sanin mai shago mai lamba 64 sai aka ce ba a san inda yake ba. Mun bincika shago mai lamba 67 bamu ga koma ba, amma da aka shiga shago 64 sai aka ga makudan kudi a cikin jakunkunan 'Gana-Must-Go".

EFCC ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike domin gano mutumin da ya mallaki kudin da kuma inda ya same su.

Labarai masu alaka