Annobar sankarau ta bulla a Ghana

Gwamnatin shugaba Nana Akufo Addo ta dauki kwararan matakan hana yaduwar cutar sankarau Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin shugaba Nana Akufo Addo ta dauki kwararan matakan hana yaduwar cutar sankarau

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Ghana, sun tabbatar da bullar cutar sankarau a jihar Ashanti, inda rahotannin ke cewa dalibai hudu na wata babbar sakandire sun mutu sanadiyar kamuwa da cutar.

Rahotanni sun ce a makon da ya gabata ne cutar ta bulla, amma daliban makarantar ba su fahimci wacce irin cuta ce ba.

Hakan ne kuma ya har zuka su suka fara hayaniya ganin cewa dalibai 26 sun kamu da wani ciwo har hudu daga cikinsu sun mutu.

Daga bisani ne mahukunta a makarantar suka gudanar da bincike domin gano wacce irin cuta ce, a inda kuma daga karshe suka gano cewa sankarau ce.

Wannan dalilin bullar cutar a makarantar da ke jihar ta Ashanti, ya sa an rufe ta na wucin gadi.

Tuni kuma mahukunta suka fara wayar da kan jama'ar gari a kan su kiyaye da yanayin da ake ciki na zafi, domin gujewa kamuwa da cutar ta sankarau.

Kazalika gwamnatin jihar ta kuma samar da allurar rigafin cutar da magunguna a asibitoci tare da samar da cibiyoyin kula da cutar.

Yanzu haka dai daga cikin dalibai 26 da suka kamu da cutar, an sallami 19 daga asibiti, a inda hudu suka mutu, yayin da kuma sauran ke cigaba da karbar magani.

A bara ma dai cutar sankarau din ta bulla a kasar, inda mutum kusan 500 suka kamu da ita, abin da ya janyo mutuwar 100 daga cikinsu.

Labarai masu alaka