Senegal: An yi zanga-zanga a kan garkame 'yan hamayya

Shugaba Macky Sall na fuskantar suka a kan matakin garkame 'yan adawa
Image caption Shugaba Macky Sall na fuskantar suka a kan matakin garkame 'yan adawa

Dubban 'yan kasar Senegal sun yi zanga-zanga a babban birnin kasar, Dakar, domin nuna rashin amincewarsu ga shugaban kasar, Macky Sall kan garkame masu hamayya.

Masu zanga-zangar dai na neman shugaban kasar, Macky Sall ya saki abokan hamayyarsa da ke garkame a gidan yari da suka hada da magajin garin birnin Dakar, Khalifa Sall.

Khalifa Sall dai ya kwashe watanni a kurkuku bisa zarge-zargen zamba cikin aminci da wadaka da kudin gwamnati.

Ana dai yi wa magajin garin kallon wani mutum daya tilo da ka iya jan daga da shugaba Macky Sall a lokacin babban zaben kasar da za a yi a 2019.

Kungiyar da ta yaki tazarcen tsohon shugaban kasa, Abdoulaye Wade ta Fed Up Youth Movement ce ta shirya wannan zanga-zanga.

Labarai masu alaka