Saudiya za ta gina birnin nishadi a kusa da Riyadh

King Salman bin Abdulaziz Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiya

Saudiya ta na shirin gina abin da ta bayyana a matsayin birnin nishadi a wajen babban birnin kasar, Riyadh.

A shekarar 2022 ake sa ran bude birnin, a inda za a rinka bukukuwan baje kolin al'adu, da wasanni da kuma abubuwan shakatawa.

Mataimakin yarima mai jiran gado a Saudiya, Mohammed bin Salman ya ce ana fatan birnin da za a gina, zai zama wani wuri mai muhimmanci ga raya al'adu da cimma bukatun mutane masu tasowa a kasar a gaba.

Gwamnatin Saudiya na fatan wannan shiri da ake wa lakabi da Vision 2030, zai samar da guraben ayyukan yi ga matasa a kasar, tare da yin sassauci ga wasu tsauraran ka'idoji a kasar.