Uganda: An kama matar da ta soki uwar-gidan Museveni

Uganda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daga gefen hagu, mataimakin Sifeta Janar na 'yan sandan Uganda Andrew Kaweesi

'Yan sanda a Uganda sun tabbatar da kama wata malamar jami'a wadda ta soki matar shugaban kasar Yoweri Museveni a shafin sada zumunta.

Wani kakakin 'yan sanda, Emilian Kayima ya ce ana tsare da malamar jami'ar kuma mai fafutuka, Stella Nyanzi.

Mista Kayima ya ce an tuhumi malamar da aikata laifin aibanta uwargidan shugaban kasar ta intanet.

A farkon watan nan ne Ms Nyanzi ta soki ministar ilimi ta kasar, wacce ita ce matar shugaban kasar, Janet Museveni, bayan gwamnati ta kasa cika alkawarin da ta yi wa 'yan mata a kasar.

Alokacin yakin neman zabe, gwamnatin ta yi alkawarin samar da audugar mata kyauta ga yara mata wadanda ba su da karfin siyan audugar mai tsafta.