Mutanen gari sun far wa 'yan gudun hijira a Izmir

Syria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu 'yan gudun hijirar Syria a Turkiya

Daruruwan 'yan gudun hijiran Syria dake Turkiya, sun gudu daga sansanin wucin gadi da suke zama a lardin Izmir, bayan mutanen garin sun far musu.

Sa'insa tsakanin su ta ci gaba da yaduwa ne, bayan iyayen wani yaro 'yan asalin lardin, sun diran ma sansanin 'yan gudun hijirar saboda sun ce 'yan Syria sun bugi yaron na su.

Daga nan ne mutane da yawa 'yan asalin yankin dauke da wukake da kulake, suka far ma 'yan gudun hijirar.

Daga baya kuma, wasu daruruwan mutanen garin suka lalata tanti-tanti na 'yan gudun hijirar tare da cinna musu wuta.

Mutane talatin ne aka tabbatar sun jikkata, daya daga ciki yana mawuyacin yanayi.

Miliyoyin 'yan gudun hijirar Syria ne ke zaune a Turkiya--adadin da ya haura na ko ina a duniya.