An kara kudin kujerar Hajji a Kamaru

Ana sa ran maniyyata 3,500 ne za su je sauke faralli a bana daga Kamaru Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana sa ran maniyyata 3,500 ne za su je sauke faralli a bana daga Kamaru

Ma'aikatar harkokin cikin gida a Kamaru mai kula da tsara safarar maniyyata zuwa aikin hajji, ta fitar da sanarwa in da ta ke shaida wa maniyyatan bana cewa kudin kujerar Makkah ya karu da jaka dari biyu da tamanin da biyu (282.000 FCFA).

Wannan karin ya biyo bayan faduwar da dala ta ke yi, da bullo da wani sabon tsarin da aka yi a Arafat, da kuma karin kudin Otel

Tuni dai ma'aikatar ta bayar da umarnin fara yiwa maniyyatan bana rijista.

A bana ma dai kamfanin jirgin saman kasar ta Kamaru wato Camair-Co da hadin gwiwar na kasar Saudiyya Flynas ne za suyi jigilar alhazan zuwa kasa mai tsarki.

Ana dai bukatar adadin alhazan bana daga Kamaru 3,500, dan haka hukumar kula da alhazan kasar ta bukaci duk wani maniyyaci da ya yi kokarin kammala biyan kudin kujerarsa kafin ranar 15 ga watan Yuni na shekarar da muke ciki.

Hukumar ta ce idan har aka samu adadin da ake bukata na alhazan , to za a rufe biyan kudin kujera a kasar.

Har ila yau kuma, wata sanarwar daga ministan harkokin cikin gidan kasar ta Kamaru, ta dakatar da wasu mutane shida daga cikin jerin wadanda suke jigilar maniyyata saboda saba ka'idojin da suka yi.

Labarai masu alaka