'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda da sojoji a Lagos

Sojoji na cikin wadanda aka kashe Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojoji na cikin wadanda aka kashe

Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu mutane da ake zargi 'yan bindiga ne sun kashe jami'an tsaro bakwai a birnin Lagos da ke kudu maso yammacin kasar.

Rahotannin sun kara da cewa 'yan bindigar sun kai hari ne a unguwar Isawo da ke yankin Ikorodu, inda suka kashe sojoji biyu da 'yan sanda bakwai.

Ganau sun ce masu tayar da kayar bayan sun mamaye unguwar da safiyar ranar Lahadi.

Sun ce sun kashe jami'an tsaron ne bayan sun yi musu kwanton-bauna.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Olarinde Famous-Cole wanda ya tabbatarwa BBC da aukuwar lamarin, ya ce har yanzu ba su da kiyasin mutanen da suka mutu.

Wani mutum da ya shaida abin da ya faru a yankin ya ce, "Mutanen suna fito da bindigogi sannan su yi wa mazauna unguwar fashi. Yanzu mazauna wannan yanki suna cike da fargaba."

A shekarar 2016 an kashe mutane da dama a unguwar ta Isolo bayan fafatawar da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga, lamarin da ya tilasta wa hukumomi girke karin jami'an tsaro a yankin.

Labarai masu alaka