Harin bom da mota ya halaka mutane 15 a Somalia

somalia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Al-Shabaab ta ce mayakanta ne suka kaddamar da harin

Wani harin bom da mota, wanda aka yi hakkon babban hafsan sojojin Somaliya, ya halaka akalla mutane 15 a Mogadishu babban birnin kasar.

Maharin ya tuka wata mota dake makare da bama-bamai, inda ya tunkari kwambar motocin dake dauke da Mohamed Ahmed Jimale, wanda aka nada a makon jiya.

Wani jami'in soja ya ce motar ta kasa kai wa ga kwambar motocin babban hafsan sojin, a inda ta tarwatse a jikin wata karamar motar bus.

Akasarin wadanda suka mutun fasinjojin motar bus din ne.

Kungiyar Al-Shabaab ta ce mayakanta ne suka kai harin, wanda shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin hare-haren da ake kai wa cikin kwanaki biyar da suka wuce.