An kori daruruwan mutane daga gidajensu a Lagos

Lagos Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ire-iren gidajen al'ummomin dake bakin ruwa a Lagos

A Najeriya, 'yan sanda sun tilasta wa daruruwan mutane barin gidajensu a jihar Lagos.

Gwamnatin jihar ce take gudanar da aikin rushe gidajen al'ummomi da ke bakin ruwa a yankin Lekki, ta hanyar cinnawa gidajen wuta.

Akasarin mutanen da aka tilasata ma barin gidajen na su, sun yi cirko-cirko ne akan jiragen ruwa, suna kallon gidajensu na ci da wuta.

Wani wanda ya shaida lamarin ya ce da sanyin safiya ne 'yan sanda suka dira a yankin inda suka rika harba hayaki mai sa hawaye, tare da tilasta ma mutane tserewa ta jiragen ruwa.

Ganau din ya yi zargin cewa yayin da mutanen ke guduwa ne, 'yan sanda suka yayyafa wa gidajensu kalanzir, inda suka cinna musu wuta.

Rahotanni sun ce an harbi matasa biyu, kuma daya daga cikinsu ya mutu saboda harsashi ya same shi a wuya.

Wata kungiyar taimakon jama'a, Justice and Empowerment Initiative ta ce 'yan sanda sun tabbatar mata cewa gwamnatin jihar ce ta basu umurnin korar mutanen daga yankin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu mazauna unguwanni bakin ruwa lokacin wata zanga-zanga a can baya

Wannan ne karo na hudu a cikin makonni uku da gwamnatin jihar Lagos din ke yunkurin korar mutanen dake zama a kusa da ruwa.

Ana zargin gwamnatin da yinkarfa-karfa wajen kwace wa talakawa filayensu domin ba attajirai.

Mazauna yankin sun ce gwamnatin ta na gudanar da aikin rusau din ne duk da umurnin kotu da ya dakatar da haka.

Sai dai gwamnatin ta ce an shafe shekaru a na gargadin mutanen da su kaurace wa yankin amma sun ki ji.

A halin yanzu dai, babu wani tanadi da aka yi wa mutanen da aka raba da gidajensu.