An gano malaman bogi a Nijar

Gwamnatin Nijar na kashe makudan kudade a bangaren ilimi
Image caption Gwamnatin Nijar na kashe makudan kudade a bangaren ilimi

A jamhuriyar Nijar, matsalolin da suka dabai baye fannin illimi na cigaba da tayar da hankalin al'ummar kasar.

A kan hakan ne 'yan majalisar dokokin kasar suka kira ministan cikin gida, kuma shugaban kwamitin shiga tsakanin gwamnati da malaman makarantu, Bazoum Muhammad domin ya yi musu karin bayani a kan wannan batu.

Ministan Bazoum Muhammad ya yi wa majalisar bayani in da ya ce gwamnatin kasar na asarar a kalla kudaden sefa miliyan hudu a duk shekara a bangaren ilimi.

Sannan kuma, an gano malaman bogi kusan dubu uku da ake daukar kudinsu ba tare da sun yi aiki ba.

'Yan majalisar sun ce, bisa la'akari da bayanin da ministan ya yi musu, suna kira ga iyayen yara da su farka, domin kuwa wannan matsala ba gwamnati kadai ta shafa ba, har da su.

Daga bisani 'yan majalisar, sun nuna gamsuwar su kan yadda gwamnatin tace ta na kokari wajen ceto wannan fanni.

Amma kuma ta kara jan hankalin gwamnatin da kada ta gaza, ta cigaba da kokari dan tabbatar da bangaren ilimin ya inganta.

Kuma gwamnatin ta yi kokari wajen bankado malaman bogi, dama wadanda ba kwararru ba.

Labarai masu alaka