Ana son raba Rasha da Syria

Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Syria da Rasha
Image caption Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Syria da Rasha

Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya isa Italiya domin halartar taron ministocin kungiyar kasashe bakwai da ke da karfin tattalin arziki ta G7.

Ana kyautata tsammanin taron zai mayar da hankali a kan yadda za a matsawa Rasha ta nisanta kanta da ga shugaba Bashar Al-Assad na Syria.

Tun dai feshin iska mai guba da aka ce gwamnatin Syria ta yi kan yankunan da 'yan tawaye ke rike da su a kasar, al'amarin da ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar fararen hula da dama, kasashe masu fada aji suke ta faman kwafa kan alakar Rasha da gwamnatin Syria.

Sakataren harkokin wajen Amurka ,Rex Tillerson ya kalubalanci Rasha bisa gaza hana afkuwar harin makami mai guba da Syria ta kai kan fararen hula..

Mista Tillerson, ya kuma kara da cewa a har kullum babban burin Amurka shi ne samun galaba a kan kungiyar jihadi ta I S.

A makon da ya gabata ne dai Amurka ta dauki matakin kai harin makami mai linzami guda 51 zuwa sansanin jiragen kasar Syria da ake tsammanin daga nan ne aka kyankyashe shirin kai harin iska mai guba kan fararen hula.

Labarai masu alaka