Gwamnatin Lagos ta musanta kashe mutane a yankin marasa galihu

Lagos Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ire-iren gidajen al'ummomin da ke bakin ruwa a Lagos

Gwamnatin jihar Legas ta musanta rahotannin da ke cewa ta kori marasa galihu daga matsugunansu da kkarfin tuwo.

Kwamishinan yada labaran jihar, Steve Ayorinde, ya shaida wa BBC cewar rundunar tabbatar da zaman lafiya a jihar ce ta ruguje wuraren da aka gina kan hanyar ruwa ba bisa ka'ida ba, wadanda suka zama mafaka da kuma hanya ga 'yan fashi da masu garkuwa da mutane da kuma masu tada kayar baya.

Kwamishinan ya kara da cewar rundunar tabbatar da zaman lafiyar ta yi aiki ne a ranar Lahadi, yayin da rahotannin da ke cewa an kashe mutane kuma suka ce hakan ya faru ne ranar Asabar.

Ayorinde ya ce 'yan sanda sun alakanta mutuwar da rikicin kabilanci tsakanin Yarbawa da 'yan kabilar Egun.

Rahotanni dai sun ce gwamnatin ta jihar Legas ta gudanar da aikin rushe gidajen al'ummomi da ke bakin ruwa a yankin Lekki, ta hanyar cinnawa gidajen wuta.

Akasarin mutanen da aka tilasata wa barin gidajen nasu, sun yi cirko-cirko ne a kan jiragen ruwa, suna kallon gidajensu na ci da wuta.

Wani wanda ya shaida lamarin ya ce da sanyin safiyar jiya Lahadi ne 'yan sanda suka dira a yankin inda suka rika harba hayaki mai sa hawaye, tare da tilasta wa mutane tserewa ta jiragen ruwa.

Ganau din ya yi zargin cewa yayin da mutanen ke guduwa ne, 'yan sanda suka yayyafa wa gidajensu kalanzir, inda suka cinna musu wuta.

Rahotanni sun ce an harbi matasa biyu, kuma daya daga cikinsu ya mutu saboda harsashi ya same shi a wuya.

Amma kwamishina labaran jihar ta Legas din ya ce babu wanda ya yi harbi tsakanin rundunar tabbatar da zaman lafiya da kuma 'yan sanda, yayin da ya kara da cewar rundunar 'yan sandan jihar na bincike kan kisan.

Kwamishinan ya ce gidajen da aka rusa suna kan filin wani iyali ne wanda wata kotu ta bai su iko kan filin. Saboda haka filin ba na gwamnatin jihar Legas ba ne.

A ranar Lahadi wata kungiyar taimakon jama'a, Justice and Empowerment Initiative ta ce 'yan sanda sun tabbatar mata cewa gwamnatin jihar ce ta basu umurnin korar mutanen daga yankin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu mazauna unguwanni bakin ruwa lokacin wata zanga-zanga a can baya

Wannan ne karo na hudu a cikin makonni uku da gwamnatin jihar Lagos din ke yunkurin korar mutanen da ke zama a kusa da ruwa.

Ana zargin gwamnatin da yin karfa-karfa wajen kwace wa talakawa filayensu domin ba attajirai.

Mazauna yankin sun ce gwamnatin ta na gudanar da aikin rusau din ne duk da umurnin kotu da ya dakatar da haka.

Sai dai gwamnatin ta ce an shafe shekaru ana gargadin mutanen da su kaurace wa yankin amma sun ki ji.

A halin yanzu dai, babu wani tanadi da aka yi wa mutanen da aka raba da gidajensu.

Labarai masu alaka