Za a daure makiyayan da suka sace Olu Falae

Herdsmen Hakkin mallakar hoto STEFAN HEUNIS
Image caption An samu makiyayan da laifin garkuwa da tsohon sakaren gwamnatin tarayyar Najeriya, Olu Falae.

Wata Kotu a Najeriya ta yanke wa wasu mutane hukuncin daurin rai da rai bayan samunsu da laifin yin garkuwa da tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Cif Olu Falae.

Babbar kotun da ke jihar Ondo wanda Mai shari'a, Williams Olamide, ke jagoranta ce ta yanke wa makiyaya bakwai hukuncin a ranar Litinin.

Ko da yake suna da damar daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke musu.

An yi garkuwa da Olu Falae ne a ranar 21 da watan Satumbar shekarar 2015, a lokacin da ya ke bikin cika shekara 77 da haifuwa.

Sai dai bayan 'yan kwanaki wadanda suka yi garkuwan da shi sun sake shi bayan an biya su kudin fansa.