BH: Sojoji sun saki mutum 593 da suke tsare da su

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram ta koma kai harin sari-ka-noke

Rundunar sojin Najeriya ta sallami wadansu mutane 593 ciki har da mata da kananan yara, bayan rashin samunsu da alaka da Kungiyar Boko Haram.

Dubban mutane ne dai ke tsare a hannun dakarun kasar a yakin da suke yi da Boko Haram.

Babban Hafsan Sojin Kasa, Tukur Buratai shi ne ya ba da umarnin "Sakin mutanen ba tare da gindaya wani sharadi ba, idan har ba su da wata dangantaka da masu ta da kayar baya ko kuma Boko Haram."

Birgediya Janar, Abdulraman Kuliya ya bayyana cewa mutanen da aka sakin a ranar Litinin kuma an mika su ne ga gwamnatin Jihar Barno.

A cewarsa an kama mutanen ne a wurare daban-daban kuma lokutan da suka kwashe a tsare ya bambanta.

Hare-haren Boko Haram ya karu tun bayan karshen daminan bara, ko da yake galibi ana dakile hare-haren ko kuma harin ya tsaya a kan 'yan kunar bakin waken kadai.

Ko a karshen makon jiya ma wasu 'yan mata sun kai harin kunar bakin wake a wani masallaci a garin Maiduguri, inda bam din da suke dauke da shi ya tashi da su kafin su kutsa cikin masallacin.