'An samu ƙaruwar mutanen da ake yanke wa hukuncin kisa a Nigeria'

Kungiyar Amnesty International

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyar Amnesty International ta ce kasar China ita ce kan gaba a duniya wajen zartar da hukuncin kisa a shekara a 2016

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta duniya, Amnesty International ta fitar da rahoton shekara ta 2016 kan zartar da hukuncin kisa a duniya

A cikin rahoton Amnesty ta ce an samu gagarumar raguwar mutanen da aka zartar wa hukuncin kisa a faɗin duniya.

Sai dai Amnesty ta ce ko da yake an samu wannan sauyi, amma ba haka abin yake a China ba, wadda ƙungiyar ta zarga da zartar da gagarumin hukuncin kisa.

Ta ce mutanen da China ta zartar musu da hukuncin kisa a bara sun haura na sauran ƙasashen duniya idan aka haɗe su wajen guda.

Sai dai a karon farko cikin sama da shekara goma, Amurka ba ta cikin ƙasa biyar da suka fi amfani da hukuncin kisa a shekarar da ta gabata.

China dai ta zartar da hukuncin kisa a kan sama da mutum dubu daya a faɗin ƙasar.

Yayin da Iran ke biye da ita da adadin mutane sama da 567.

Sai kuma Saudi Arabia wadda ita ce ƙasa ta 3 a cikin rahoton Amnesty inda ta zartar da hukunci a kan sama da mutum 154.

Ƙungiyar ta ce a Nijeriya mutum uku ne aka yi wa hukuncin kisa a shekarar ta 2016.

To sai dai, rahoton ya ce bayan kasar China, Nijeriya ita ce ƙasa mafi yawan mutanen da kotuna suka yanke wa hukuncin kisa, inda kungiyar ta ce yawan mutanen ya kai 527.

Bayan Nijeriya da ke kan gaba a ƙasashen Afirka sai kuma Masar wadda ta yanke wa mutum 237 hukuncin a kashe su.

Kamaru na da mutum 160, yayin da kasar Zambia rahoton ya ce ta yanke wa mutum 101 hukuncin cewa a kashe su.

Jamhuriyar Nijar kuma in ji rahoton Amnesty, ta yanke wa mutum 11 hukuncin kisa a shekarar ta 2016.